Takaitaccen tarihin kwallon Ghana

'yan kwallon Ghana
Image caption Wasu 'yan kwallon Ghana

Ghana ta kasance kasar Afrika ta farko da ta samu a gurbi a gasar cin kofin duniya da za ayi a Afrika ta Kudu abinda kuma yasa ta kagara lokaci yayi a fara gasar don ta nuna kanta a idon duniya.

Tawagar Black stars ta kasar Ghana dai ta kafa tarihi a gasar da aka yi a Jamus a shekara ta 2006 inda ta zira kwallo cikin dakikoki 68 a wasan data doke jamhuriyar Czech daci 2 da 1 amma duk da haka Ghanar bata wuce zagayen na biyu ba.

Karfin tawagar Black stars dai ya ragu ganin cewar shahararren dan wasanta dake taka leda a Chelsea wato Micheal essien ba zai taka mata leda ba lokacin gasar a Afrika ta kudu saboda rauni amma dai akwai irinsu sulley Muntari da Asamoah Gyan da kuma Ricahrd Gkingston wadanda zata sawa ido.

Kalubalen dake gaban kocin kasar Milovan Rajevac dai shine ya kai matakin akalla zagayen kusada karshe a Afrika ta Kudu ganin cewar matasan Ghana 'yan kasada shekaru 20 sun lashe kofin duniya a bara.

Ghana na rukunin da tare da kasashen Jamus, Serbia da kuma Australia.