Drogba zai jagoranci Ivory Coast zuwa Afrika ta Kudu

Drogba
Image caption Dan wasan Chelsea Drogba yana cikin wadanda za aso aga taka rawarsu a Afrika ta Kudu

An cire sunayen Bakary Kone da Kanga Akale daga cikin jerin 'yan wasan da zasu wakilci Ivory Coast a gasar cin kofin duniya.

Sai dai Didier Drogba, Salamon Kalou, Aruna Dindane da Seydou Doumbia suna cikin wadanda zasu taka leda a Afrika ta Kudu.

Kocin kasar Sven-Goran Eriksson ya koma saka Daniel Yeboah a matsayin dan wasa daya tal da za a murza ledar da shi.

Ivory Coast na rukunin Ga tare da kasashen Brazil da Portugal da Koriya ta Arewa.

Cikakken jerin 'yan wasan Ivory Coast:

Masu tsaron gida: Boubacar Barry (Lokeren, Belgium), Aristides Zogbo (Maccabi Netanya, Israel), Daniel Yeboah (Asec, Ivory Coast).

Masu buga baya: Souleymane Bamba (Hibernian, Scotland), Arthur Boka (VB Stuttgart, Germany), Benjamin Brou Angoua (Valenciennes, France), Guy Demel (Hamburg SV, Germany), Emmanuel Eboue (Arsenal, England), Steve Gohouri (Wigan Athletic, England), Siaka Tiene (Valenciennes, France), Kolo Toure (Manchester City, England).

Masu buga tsakiya: Jean-Jacques Gosso Gosso(Monaco, France), Abdelkader Keita (Galatasaray, Turkey), Emmanuel Kone (International Curtea Arges, Romania), Gervinho (Lille, France), Koffi N'Dri Romaric (Sevilla, Spain), Cheik Ismael Tiote (Twente Enschede, Holland), Yaya Toure (Barcelona, Spain), Didier Zokora (Sevilla, Spain).

Masu buga gaba: Aruna Dindane (Lekhwiya, Qatar), Didier Drogba (Chelsea, England), Salomon Kalou (Chelsea, England), Bakary Kone (Olympique Marseille, France).