Takaittaccen tarihin Koriya ta arewa

Koriya ta arewa ta yi ba zata a nahiyar Asiya, saboda sai a ranar karshe ne ta samu damar tsallakewa domin taka leda a gasar cin kofin duniya ta bana.

A wasannin cacantar taka leda a gasar da kasar ta buga a nahiyar Asiya, zagaye na hudu, kasar ta lashe wasanni uku ne sanan aka doke ta a wasanni biyu a yayinda ta buga kunnen doki a wasanni uku.

Koriya ta arewa dai ta buga wasan dab da kusa dana karshe ne a gasar da aka shirya a Ingila, a shekarar alif dari tara da sittin da shida. Kuma ta kai wanan matakin ne bayan tan doke manya kasashe a gasar daga ciki ma har da Italiya.

Tun bayan lokacin dai kasar bata sake halarta wata gasa ba. Za'a iya cewa kusa kashi biyu cikin uku na 'yan wasan kasar na taka leda ne a kungiyoyin cikin gida a kasar.

Kasar dai tana ji ne da dan wasan ta da ke takawa kungiyar FC Rostov leda wato Hong Yong-Jo, kuma Kim Jonh Hun ne zai jagoranci tawagar kasar zuwa gasar da za shirya a kasar Afrika ta kudu a matsayin kocinta.

koriya ta arewa dai za ta gwabza ne a rukunin G tare da Kasar Brazil da Portugal da kuma Ivory Coast.