Takaittaccen tarihin Paraguay

'yan wasan Paraguay
Image caption Paraguay a wani wasa da ta buga da Argentina

Kasar Paraguay ta halarci gasar cin kofin duniya sau bakwai a baya, kuma gasar da za ta halarta a kasar Afrika ta kudu shine zai zama na hudu da kasar ke halarta a jere.

A gasar da kasar ta halarta a Jamus a shekarar dubu biyu da shida, an tsige ta ne a zagayen farko.

Kasar dai bata taba lashe wasanni biyu a jere a gasar ba, kuma bata taba tsallake zagayen farko ba.

Tarihi ya nuna cewar a gasa bakwai da kasar ta halarta a baya ta lashe wasanni biyu ne, sai ta buga kunnen doki a biyu, sannan kuma aka doke ta a wasanni tara.

A wasannin cancantar taka leda a gasar cin kofin na bana Paraguay ta taka rawar gani a wasanni da ta buga a kudancin Amurka, saboda ta lashe wasanni goma ta kuma buga kunnen doki a wasanni uku, yayinda aka doke ta a wasanni biyar.

Paraguay na da shahararun 'yan wasa kamar su Roque Santa Cruz wanda ke takawa kungiyar Manchester City leda ta kasar Ingila da kuma Oscar Cardozo.

Dan kasar Argentina Gerardo Martino ne zai jagoranci tawagar kasar zuwa gasar da za a shirya a kasar Afrika ta kudu a matsayin kocinta.

Paraguay dai za ta buga ne a rukunin F tare da kasar Italiya da Slovakia da kuma New zealand.