Takaittaccen tarihin Spain

'Yan wasan Spain na murnan zura kwallo
Image caption 'Yan wasan Spain na murnan zura kwallo

Spaniya dai ta nuna gogewarta a harkar tamoula, a yayinda ta lashe duk wasannin da ta buga a wasan cancantar taka leda a gasar da za a shirya a kasar Afrika ta kudu.

Kasar dai ta zura kwallaye ashirin da takwas ne a wasannin da ta buga a yayinda aka zura mata biyar.

Tarihi ya nuna cewar Spaniya ta halarci gasar cin kofin duniya sau goma sha biyu, kuma tun bayan gasar da ta halarta a shekarar 1974, bata taba fashin halartar wata gasa ba ya zuwa yanzu.

Gasar da Spaniya ta fi fice a gasar cin kofin duniya, ita ce gasar da ake shirya a Brazil, a shekarar 1950 inda ta kare a matsayin ta hudu.

Spaniya dai za ta halarci gasar cin kofin duniya na bana ne da manyan 'yan wasanta, kamar su David Villa da Fernando El nino Torres da kuma Xavi Hernandez. Vicente del Bosque ne zai jagoranci tawagar kasar a matsayin kocinta.

Spain dai za ta buga ne a rukunin H, tare da Switzerland da Honduras da kuma Chile.