Mai yiwuwa Drogba ba zai taka leda a Afrika ta Kudu ba

Didier Drogba
Image caption Didier Drogba na daga cikin wadanda ake saran za su haskaka

Da alamu kyaftin din Ivory Coast Didier Drogba ba zai taka leda a gasar cin kofin duniya da ake shirin farawa a Afrika ta Kudu ba, bayanda ya karye a kafa.

Dan wasan wanda ke da shekaru 32, ya samu raunin ne mintina 16 da fara wasan sada zumunta tsakanin kasar sa da Japan, bayan da yaci karo da Marcus Tulio Tanaka.

Sai dai kociyan kasar Sven-Goran Eriksson, yace har yanzu suna sa ran dan wasan zai taka leda a gasar ta bana. "Har yanzu ba mu da tabbas, komai zai iya faruwa," inji Ericksson

Ya kara da cewa: "babban rauni ne, amma ban san yanayin sa ba, hakika na damu, shi kyaftin, kuma daya daga cikin manyan 'yan wasan mu".