Mihajlovic ne sabon kociyan Fiorentina

Sabon kociyan Fiorentina
Image caption Sabon kociyan Fiorentina

Kungiyar Fiorentina ta nada Sinisa Mihajlovic, a matsayin sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar.

Mihajlovic wanda tsohon dan wasan Serbia ne, ya maye gurbin Cesare Prandelli, wanda zai karbi tawagar Italiya da zarar an kammala gasar cin kofin duniya. Shi dai Mihajlovic, wanda ya ajiye mukaminsa na kocin Catania, an dade ana alakanta shi da kungiyoyin Inter Milan da kuma Fiorentina.

Wata sanarwa da ta fito daga shafin Intanet na klub din, tace a ranar Asabar ne za a gabatar da sabon kociyan a filin wasa na Stadio Artemio Franchi da ke birnin Florence.