Takaitaccen tarihin kwallon Holland

Tawagar 'yan wasan Holland
Image caption Tawagar 'yan wasan Holland

Babban abinda ke gaba Holland dai shi ne na ganin ta farfado da kimarta a fagen kwallon kafa a duniya, tun bayan mummunar rawar da ta taka a gasar cin kofin nahiyar Turai a shekara ta 2008.

Kasar dai ta halacci gasar cin kofin duniya sau takwas, inda takai wasan karshe har sau biyu.

Holland na cikin tsirarun kasashen da suka lashe baki dayan wasannin da suka buga a kan hanyar su ta zuwa Afrika ta Kudu.

Inda ta lashe wasanni takwas din da ta buga, yayinda aka zira mata kwallaye biyu kacal. Daga cikin manyan 'yan wasan da kasar ke saran dogara da su a Afrika ta Kudu sun hada da Wesley Sneijder wanda ya tallafawa Inter Milan ta lashe gasar zakarun turai.

Da Arjen Robben da kyaftin Mark Van Bommel na Bayern Munich da kuma Robin Van Persie an Arsenal.

Kuma za su fafatane a rukunin E da kasashen Denmark da Japan dakuma Jamhuriyar Kamaru.

Masana da dama na yiwa kasar kallon daya daga cikin wadanda za su taka rawa ta azo agani.