Takaitaccen tarihin kwallon Honduras

Honduras na fatan taka rawar gani a gasar ta bana
Image caption Honduras na fatan taka rawar gani a gasar ta bana

Wannan ne karo na biyu da Honduras ke halattar gasar cin kofin duniya, kuma tayi hakanne cikin mamaki abinda ya jefa dubban 'yan kasar cikin murna.

Honduras ta sha da kyar akan hanyarta ta zuwa Afrika ta Kudu, domin sai zagayen karshe sannan ta samu kanta.

Sai dai masana na jinjina mata ganin irin kasashen da fafata da su akan hanya.

Akwai babban kalubale a gaban kociya Roneildo Rueda, ganin cewa yau shekaru 28 kenan rabon kasar da wannan mataki.

Daga cikin 'yan wasan da kasar za ta dogara da su sun hada da Carlos Pavon dan shekaru 35 da David Suazo da kuma Julio Leon.

Honduras za ta fafata ne a rukunin H da kasashen Spain da Switzerland da Chile.

Kuma masu sharhi na ganin sai ta yi ta maza muddum tana son takai labari.