Liverpool na neman sabon mai horas da 'yan wasa

Rafeal Benitez
Image caption Tsohon Kociyan Liverpool, Rafeal Benitez

Kulob din Liverpool ya baza komarsa ta neman sabon mai horas da 'yan wasa bayan tsohon kociyansa Rafeal benitez ya yi sallam da shi bisa fahimtar juna a ranar Alhamis din da ta gabata.

An dai daura alhakin cefano sabon mai horas da 'yan wasan ne a kan Manajan Daraktan kulob din, Christian Purslow da tsohon shugaban kulob din Kenny Danglish.

Ana dai ganin mai horas da 'yan wasan kulob din Fulham Roy Hodgson ka iya zama dan takarar mukamin.

Sai dai tsohon mai tsaron ragar kulob din Bruce Grobbelaar da kuma tsohon dan wasan tsakiya Jamie Redknapp suna ganin tsohon shugaban kulob din Dalgish shi ne ya cancanci rike kulob din.

Dalgish dai ya rike kulob din a tsakanin shekarar 1985-1991, ya kuma ciyo wa kulob din kofi uku, kuma har yanzu ana ji da shi a Anfield saboda ya ci wa kulob din kofi shida a matsayin dan wasa.

Kuma har wa yau ana ganin yana da kusanci da kwararrun 'yan wasan kulob din.