An yi wa Drogba aikin tiyata dunduniya hannu

Didier Drogba
Image caption Didier Drogba

An yi wa Didier Drogba aiki tiyata a dunduniyan hannun sa bayan raunin da ya samu.

Har yanzu dai akwai shakku a kan dan wasan ko zai iya warkewa har ya samun damar taka leda a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan ya samu rauni a wasan da Ivory Coast ta buga da Japan a ranar Juma'a.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Ivory Coast ta ce tana da kwarin gwiwa cewar dan wasan zai samu sauki kafin a fara gasar.