Najeriya 3 koriya ta arewa 1

'Yan wasan Super Eagles
Image caption 'Yan wasan Super Eagles

A jiya ne dai Najeriya a nata shirye shiryen na halartar gasar cin kofin duniya ta buga wasan sada zumunci da Koriya ta arewa a kasar Afrika ta kudu.

Najeriya dai ta lashe wasan ne da ci uku da guda, kuma Yakubu Aiyegbeni ne yafa zura kwallon farko kafin a tafi hutu rabin lokaci.

Bayan an dawo hutun ne Najeriya ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida inda Obinna Nsofor ya zura ta biyu,bayan wasu minti biyu ne dai Koriya din ta fanshe kwallo.

Sai da aka kammala minti casa'in na wasa ana kuma cikin karin lokaci ne Obafemi Martins ya zura ta uku.