Mikel ba zi buga gasar cin kofin duniya ba

John Obi Mikel
Image caption John Obi Mikel

Dan wasan Najeriya John Mikel Obi ba zai taka leda a gasar cin kofin duniya ba saboda raunin da yake fama da shi a gwiwarsa.

A yanzu haka dai Mikel tare da Michael Essien da kuma Michael Ballack duk wadanda ke taka leda a kungiyar Chelsea ba za su taka leda ba a gasar cin kofin duniya ba.

Haryau akwai shakku akan Drogba shima saboda raunin da ya samu a wasan sada zumunci da Ivory Coast ta buga da Japan..

An yi wa Mikel aikin tiyata a gwiwarsa a watan Mayun data gabata amma har yanzu dan wasan ba zai samu sauki ba.

Brown Ideye, wanda ke taka leda a kungiyar Sochaux ta kasar Faransa ne zai maye gurbin Mikel.