Akwai shakku akan Muntari

Sulley Muntari
Image caption Dan wasan Ghana Sulley Muntari

Kocin Ghana Milovan Rajevac ya ce akwai shakku cewar dan wasan kasar Sulley Muntari zai taka leda ba a gasar cin kofin duniya saboda ba shi da isashen lafiya. Rashin Muntari a tawagar Ghana na iya kawo babban koma bayan ga tawagar kasar, saboda kyaftin din tawagar, Micheal Essien shima ba zai samu damar halarta gasar cin kofin duniyan ba.

Masana na ganin kwarewar Muntari a harkar tamoula zai taimakawa tawagar Ghanan saboda yawanci 'yan wasanta matasa ne da ba su da kwarewa sosai.

Sulley Muntari dai ya samu raunin ne a cinyarsa a wasan sada zumunci da Ghana ta buga da Latvia a ranar talatar da ta gabata.

A yanzu haka dai likitoci na duba lafiyarsa domin ganin ko dan wasan zai iya taka leda a kasar Afrika ta Kudu.