Brazil ta doke Tanzaniya da ci 5-0

Kaka na daga cikin 'yan wasan da Brazil ke ji da su
Image caption Kaka na daya daga cikin 'yan wasan da Brazil ke ji da su

Brazil ta lallasa Tanzania da ci biyar da nema a wasan sada zumuncin da suka buga a birnin Darel-Salam.

A ci gaba da shirye-shiryen da Kasashe ke yi domin tunkarar gasar cin kofin duniya da za a fara a ranar juma'a a Afrika ta kuda.

Robinho na daya daga cikin wadanda suka zira kwallo a wasan, inda ya zira kwallaye biyu, sai Kaka da shi ma ya zira kwallo guda.

Ita ma dai Ingila ta buga wasan sada zumunci da wata kungiyar cikin gida a kasar Afrika ta Kudu mai suna Platinum Stars, inda Ingila din ta doke kungiyar da ci uku da nema.

Joe Cole da Roony na daya daga cikin wadanda suka zira kwallaye a wasan.