'Yan kallo sun ji rauni a Afrika ta kudu

'yan kallo
Image caption An samu radani wajen shiga filin wasa

'Yan kallo goma sha shida ne suka jikata a wajen filin wasan da Najeriya ta kara da Koriya ta arewa a wasan sada zumunci.

An dai samu rudani ne a lokacin da ake ture turen shiga cikin filin wasa na Makhulong dake birnin Johannesburg.

An dai bar 'yan kallo ne su shiga filin wasan a kyauta, abin da kuma ya janyo sama da 'yan kallo dubu goma filin wasan.

Hukumar FIFA ta ce ba ta da hannu wajen shirya wasan, saboda haka ba za ta dauki alhakin abin da ya faru ba.

Yawancin 'yan kallon 'yan Kasar Afrika ta kudu ne da kuma 'yan Najeriya da su ka yi tattaki zuwa kasar domin kallon gasar cin kofin duniya.

Hukumar 'yan sanda a kasar ta ce 'yawancin 'yan kallon na dauke da tikitin kallon wasan kuma sunyi yunkurin balla kofar shiga filin wasan ne.

A lokacin ma da Najeriya ke wasa da Koriya ta arewa, sanda aka tsaida wasan na minti biyar saboda wani karfe da ke kare wajenzaman 'yan kallon ya balle.

Raunin da 'yan kallon su ka samu ya bar baya da kura, saboda masu ruwa da tsaki na korafi game da shirye shiryen da kasar Afrika ta kudu ta yi na karban bakoncin gasar cin kofin duniya ganin ana sauran 'yan kwanaki kafin a fara gasar.