Gasar Bundesliga ce ta fi samun riba a duniya

Ian Robben
Image caption Robben ya taimakawa bayern wajen klashe gasar ta bana

Wasu alkaluma da aka fitar sun nuna cewa gasar Bundesliga ta Jamus, itace tafin kowacce samun riba a duniya.

Hakan na nufin ta sha gaban gasar Premier ta Ingila wacce itace kan gaba a baya.

Wani rahoto da kamfanin kididdiga na Deloitte ya fitar, ya nuna cewa har yanzu gasar Premier ce kan gaba wajen samun kudaden shiga, inda take samun kusan dala biliyan uku a shekara.

Amma tace ribar su na kara raguwa saboda kashi biyu cikin uku na kudaden shigar su na tafiya ne wajen biyan albashi.

Biyan albashi na kara karuwa a mafiya yawan kasashen Turai, inda gasar Serie A ta Italiya ke kan gaba.

A kwanakin nan ne Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai UEFA, ta fitar da dokar hana kashe kudade fiye da kima, inda duk kungiyar da aka samu da laifi to za a dakatar da ita daga halattar gasar zakarun Turai daga shekara ta 2014.