Takaittacen tarihin Kamaru

Tawagar kasar Kamaru
Image caption Tawagar kasar Kamaru

Kamaru ta fara tasiri ne a gasar cin kofin Afrika tun bayan da ta halarci gasar da aka shirya a shekarar alif dari tara da casa'in a kasar Italiya inda har ta kai matakin wasan dab da kusa dana karshe.

Kamaru dai ta halarci gasar cin kofin duniya har sau biyar a tarihi.

Amma tun bayan nasarar da kasar ta samu a shekarar alif tara da casa'in a gasar, bata sake taka rawar gani ba a sauran gasar da ta halarta, yayinda ake fidda ta a zagayen farko.

A hanyar ta na zuwa gasar da za a shirya a kasar Afrika ta kudu, Kamaru ta lashe wasanni hudu, sanan ta buga kunnen doki a wasanni biyu.

Dan wasan kasar, Samuel Eto ya zura kwallaye goma sha daya a wasanni cancantar taka leda a gasar.

Paul le Guen ne kuma zai jogoranci tawagar kasar zuwa gasar da za a shirya a Afrika ta kudu.

Kuma kasar za ta buga ne a rukunin E tare da Denmark da Nertherland da kuma Japan.