Panstil ya ce Ghana za ta kai wasan kusa dana karshe

Dan wasan Ghana, John Pantsil tare da kocin kasar Milovan Rajavec
Image caption Dan wasan Ghana, John Pantsil tare da kocin kasar Milovan Rajavec

Dan wasan Ghana John Pantsil ya ce yana da karin gwiwa cewar kasarsa za ta kai wasan kusa dana karshe a gasar cin kofin duniya a kasar Afrika ta kudu.

John Pantsil wanda ya ke takawa kungiyar Fulham leda ta Ingila ya shaidawa BBC cewar kasar Afika za ta iya daga kofin duniya.

"A gasar da aka shirya a Jamus a shekarar 2006 mun kaiga bugun wasanni zagaye na biyu, kuma ganin cewa gasar ta bana za a shirya ta ne a Afika ina da kwarin gwiwa cewa za mu kai wasan kusa dana karshe". Inji Pantsil.

Ya kara da cewa wannan babban dama ce ga kasashen Afika domin su taka rawar gani.

na will be looking to build on their 2006 World Cup campaign which saw them notch up impressive