Fulham ta sayi Philippe Senderos daga Arsenal

Philippe Senderos
Image caption Tsohon dan wasan Arsenal Philipe Senderos

Fulham ta bada sanarwar siyan dan wasan bayan Arsenal Philippe Senderos na tsawon shekaru uku.

Dan wasan wanda dan asalin kasar Switzerland ne ya fara takawa Arsenal leda ne tun a shekarar 2003 bayan ya baro kungiyar Servette.

Arsenal dai ta bada aron Senderos ne ga AC Milan a kakkar wasan 2008/2009, sai kuma aka sake bada aronshi ga kungiyar Everton a kakkar wasan bara.

"Ina matukar farin cikin komawa kungiyar Fulham, saboda kungiyar na tasiri a yanzu haka". Inji Senderos a wata sanarwa daya ba shafin intanet na Fulham.