Takaitaccen tarihin kwallon Afrika ta Kudu

tawagar Afrika ta Kudu
Image caption 'yan wasan Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu wacce za ta dauki bakuncin duniya wannan ne karo na uku da za ta shiga a dama da ita a cikin gasar cin kofin duniya.

Amma dai a takarar data yi a shekarar 1998 a Faransa da kuma Koriya da Japan a shekara ta 2002, Afrika ta kudu tun a zagayen farko ake fidda ta a gasar.

Tawagar Afrika ta Kudu ana kiranta Bafana Bafana ne kuma tana da zaratan 'yan wasa kamarsu Steven Pinaar da Siyabonga Nomvete da kuma Aaron Mokoena.

Wadanda ake ganin za su yi amfani da kasancewarsu 'yan gida a gasar don share hayen 'yan kasarsu a fagen tamaular duniya.

Kocin Bafana Bafana Carlos Alberto Perriera ba bako bane a fagen kwallo a duniya ta yin la'akari da cewar shi ne ya jagoranci Brazil ta lashe kofin duniya a shekarar 1994.

Kuma a wannan karon duk da cewar Afrika ta Kudu bata da gogaggun 'yan wasa.

Amma dai ana saran kwarewarshi zai yi tasiri ga makomar kwallon kasar a bana.

Afrika ta Kudu tana rukunin A ne tare da Mexico da Urugay da kuma Faransa.