Yadda za a iya amfani da kididdigar wasannin gasar cin kofin duniya

Kididdigar wasannin gasar cin kofin duniya za ta rika nuna bayanan wasannin da ake fafatawa kai tsaye.

Me kididdigar ke nuna wa?

Kididdigar na taimakawa wajen ganin yadda wasan ke gudana a kowanne minti daga farko zuwa karshe, tare kuma da duk wasu bayanai a kan bugun daga kai sai mai tsaron gida da kuma karin lokaci.

Za a iya samun bayanai game da mahimman abubuwan da suka faru a lokacin wasa, kamar kungiyar da tafi rike kwallo, da kwallayen da aka zura, da bugun daga kai sai mai tsaron gida, da sauya 'yan wasa da sauransu. Idan ana bukatar wadannan bayanai dai za a iya amfani da manuni/alkalamin kwamfiyuta, a daura a kan alamomin da ke nuna bayanin da ake so, domin Karin bayani.

Ba a bukatar sabunta shafi, domin shafin zai kawo sabbin bayanai da kansa.

Jerin sunayen 'yan wasa

Domin sanin ‘yan wasan da za su taka leda a wasa, sai a latsa sunan kasar da ke saman taswirar.

Karin bayanai

Idan ana bukatar karin bayanai game da wasa, sai a latsa gurbin karin bayanai kan wasa dake kasan taswirarar kididdigar. Wanan sashe zai nuwa yawan ‘yan kallo da ke filin wasa, da fawul- fawul, da satar raga, da kuma firi kik, da dai sauransu.