An sabunta: 11 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 11:27 GMT

Karawa tsakanin Najeriya da Argentina

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Najeriya za ta fara fafatawa da Argentina a rukunin B, a gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu, a ranar Asabar da misalin karfe hudu agogon Najeriya.

Duka kasashen biyu dai sun sha da kyar ne akan hanyarsu ta zuwa Afrika ta Kudu.

Amma ana saran wasan zai kayatar ganin irin kwararrun 'yan wasan da suke da su.

Najeriyar dai ta halarci gasar ne ba tare da dan wasanta Mikel Obi ba, wanda yake taka leda a kulob din Chelsea, sakamakon raunin da yake fama da shi.

Kuma ana ganin hakan ka iya yima ta illa sosai.

Abinda yasa masu sharhi ke ganin Argenitana ce kan gaba, amma kiciyan Najeriya Larse Lagerback yace yaran sa a shirye suke tsaf.

Yayinda ana ta bangaren Argentina take fatan dogara kan zakaran dan kwallon duniya Lionel Messi da Diego Militto da kuma Carlos Tarvez.

Dan wasan Najeriya

Najeriya nada 'yan wasa da dama

Shi dai kociyan Argentina Diego Maradona, na fatan shiga sahun wadanda suka taba lashe gasar a matakin 'yan wasa sannan suka maimaita hakan suna masu haraswa.

Wannan rukuni na B dai ya kunshi kasashen Girka da kuma Koriya ta Kudu, wadanda za su kara a tsakanin su.

Kasashen biyu za su kara ne a ranar Asabar da daddare, bayan an kammala wasan Najeriya da Argentina.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.