Afrika ta Kudu 1-1 Mexico

Filin wasa na Soccer City
Image caption A filin wasa na Soccer City aka bude gasar

Mai masaukin baki Afrika at Kudu ta tashi 1-1 tsakanin ta da Mexico, a wasan farko na gasar cin kofin duniya ta 2010.

Mexico ce ta fara mamaye wasan da farko kafin daga bisani Afrika ta Kudu ta mike.

Babu ci dai aka tafi hutun rabin lokaci.

Amma bayan an dawo saio dan wasan Afrika ta Kudu Shabalala ya zira kwallon farko.

Sai dai aminti na 79 Marquez ya farkewa Mexico.

Kasashen biyu sunta kokarin ganin sun kara zira kwallo amma abin ya ci tura.

Tunda farko sai da aka gabatar da kade-kade da raye-raye na zamani da na gargajiya.

Bikin bude gasar dai ya samu halattar shugabannin kasashe da dama, ciki harda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon.