An sabunta: 19 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:31 GMT

Kece raini tsakani Kamaru da Denmark

Kasar Kamaru dai ta sha kaye a hannun kasar Japan da ci daya da nema, yayinda ita ma Denmark ta kwashi kashinta a hannu a karawarsu da Holland, ci biyu da nema.

Kowacce a cikin kasashen biyu dai na bukatar samun nasara a wasan na yau domin ci gaba da samun fatan kaiwa ga zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya.

Kamaru da Denmark sun taba haduwa sau biyu a wasannin sada zumunci.

Kasar Kamaru ta samu nasara a wasan farko da suka kara a shekarar 1998 da ci 2-1.

Ita ma Denmark ta rama a shekarar 2002.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.