Tsumulmular wuta domin kwallon kafa a Bangladesh

Jama'a na kallon gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya
Image caption Jama'a na kallon gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

Gwamnatin Bangladesh ta umarci kamfanonin kasar da su daina aiki da daddare domin samun isasshiyar wutar da za ta baiwa 'yan kasar damar kallon gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Umarnin ya biyo bayan mummunar zanga zangar da aka yi ne sakamakon wutar da aka dauke adaren jiya.

Wani jami'i a kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Alamgir Kabir, ya ce ankara tsaurara matakan tsaro a kamfanonin samar da wutar bayan da aka kaiwa wasu daga cikin su hari.

Yace kamfanoni za su dinga kashe wutar su har na tsawon sa'o'i biyar, yayinda aka umarci shaguna da su rufe.

Har ila yau Mista Kabir ya shawarci jama'a da su dinga kashe futulu da fankoki da na'urar dumama daki domin tattalin wutar, abinda ka iya baiwa jama'a damar kallon wasannin da ake yi a Afrika ta Kudun.

Ita dai kasar ta Bangladesh ba ta cikin kasashen da ke taka leda a gasar ta cin kofin duniya.