An sabunta: 14 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 10:24 GMT

Karawa tsakanin Holland da Denmark

A harkar tamoula, kasar Holland ta fi Denmark suna, amma karawa tsakanin kasashen biyu a baya ya zafafa.

A wasanni biyar da kasashen biyu suka buga a wasu gasa, kowace kasa ta lashe wasa biyu a yayinda suka buga canjaras a guda.

Kasashen biyu za su fuskanci matsalar amfani da zaratan ‘yan wasan su, saboda rauni. Dan wasan gaban Denmark Nicklas Bendtner na fama da rauni a yayinda akwai shakku akan mai tsaron gidan kasar Thomas Sorensen.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Kasar Holland itama dai tana fama da rashin Arjen Robben da saboda bai gama murmurewa ba daga raunin daya samu, amma dai dan wasan Real Madrid Rafeal Van der Vaart zai maye gurbinsa.

A wasanni sada zumunci da Denmark din ta buga kafin a fara gasar, ta sha kashi a hanun Austrailia da kasar Afrika ta kudu da ci daya mai ban haushi, amma kuma kasar ta doke Senegal da ci biyu da nema.

Anata bangaren dai ba’a doke kasar Holland a wani wasa ba, tun a watan Satumbar shekarar dubu biyu da tawas.

Za’a iya cewa ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.