An sabunta: 14 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:57 GMT

Karawa tsakanin Japan da Kamaru

‘Yan wasan Kamaru dai za su taka leda ne da kwarin gwiwa, ganin cewa ba a taba doke kasar ba a wasan farko a gasar cin kofin duniya.

Ita ma dai Japan tana da tarihi a kan Kamaru ganin cewa Kamaru bat a taba doke tab a. Wannan dai shine karo na farko da kasashen biyu za su taka leda a gasar cin kofin duniya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Duka kasashen biyu basu fuskanci matsala ba a wasanni cacantar taka leda a gasar cin kofin duniya, ganin cewa Kamaru c eta jagoranci rukunin da ta buga a yayinda kuma Japan ta zama ta uku a rukunin ta.

Dan wasan Kamaru Samuel Eto’o shine dan wasan da za a fi sawa ido saboda kwarewarsa kuma Itama Japan tana da Marcus Tulio Tanaka wanda dan wasan baya ne. Masana harkar kwallon kafan dai na ganin dan wasan zai iya hana Samuel Eto’o sukuni.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.