Ingila ta ce za ta rika lurra da raunin King

Ledly King
Image caption Ledley King

Za a rika lurra da yadda za ta kasance da dan wasan Ingila Ledley King bayan raunin daya samu a wasan da Ingila ta buga da Amurka a ranar asabar.

Dan wasan bai yi horo da sauran ‘yan tawagar kasar ba a ranar litinin amma kocin kasar Fabio Capello ya ce dan wasan ba zai taka leda ba a wasan da kasar za ta buga da Algeria a ranar Juma’a.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila ta ce dan wasan zai iya daukan tsawon makwanni uku ya na jinya.

Shima dai Wayne Rooney bai yi horo da tawagar kasar ba, saboda ya na fama da rauni a sahun kafarsa.

Amma dai raunin da Rooney ya samu bai yi tsananin da zai hana dan wasan taka leda ba.