An sabunta: 14 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 19:37 GMT

Karawa tsakanin New Zealand da Slovakia

Duka New Zealand da Slovakia baki ne idan ana maganar gasar cin kofin duniya, domin halartar su gasar ta bana ta baiwa jama'a mamaki.

Masana da dama na ganin wadannan kasashen a matsayin 'yan raka yarima a sha kida a rukunin F, wanda ya kunshi mai rike da kanbun Italiya da kuma Paraguay.

Wannan itace karawa ta farko tsakanin kasashen biyu a wata cikakkiyar gasa ta kasashen duniya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Daga cikin 'yan wasan da ake saran za su taka rawar gani a wasan sun hada Marek Hamsik da Shane Smeltz.

A cewar Chris Killen na New Zealand, wannan wasa ne mai matukar mahimmanci a wurin su.

Yayinda kociyan Slovania Wladimir Weiss yace za su fito gaba-gadi domin neman nasara, amma suna saran fuskantar irin wannan kalubale daga abokan karawar su.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.