Ba za’a dakatar da kakakin vuvuzela ba

Kakakin vuvuzela
Image caption Kakakin vuvuzela

Hukumar shirya gasar kwallon kafa da ake yi a kasar Afika ta kudu ta ce ba za ta dakatar da kakakin vuvuzela ba duk da korafin da ake yi.

Kakakin dai na aman sauti ne kamar kudar zuma.

Cristiano Ronaldo ya ce sautin kakakin na damun ‘yan wasa idan suna taka leda a yayinda ya ce sautin kakakin baya sa ‘yan wasan natsuwa.

Wani jam’in mai Magana da yawun hukumar y ace “Ba za’a dakatar da kakakin ba, saboda ya na cikin al’adun mutanen kasar Afrika ta kudu”.

Rich Mkhondo ya kara da cewa jama’a da dama a duniya na son kakakin vuvuzela worldwide appeal.