An sabunta: 15 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 16:23 GMT

Karawa tsakanin Brazil da Koriya ta arewa

Wasan da kasashen biyu za su buga a rukunin G shine karo na farko da suke fafatawa a tarihi.

Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyar a baya, yayinda Koriya ta arewa ce ta tamanin da biyar a duniya cikin kasashen da suka yi fice a harkar tamoula a duniya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Brazil ta halarci kowacce gasar cin kofin duniya da aka shirya a yayinda ita kuma Koriya ta kudu take halartar gasar a karo na biyu, tun bayan gasar da ta halarta a shekarar 1966.

Brazil dai ta lashe wasanni takwas cikin goma da ta buga tun bara ya zuwa yanzu a inda kuma Koriya ta kudu ta lashe wasanni biyu cikin goma sha biyu da ta buga a wannan lokacin.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.