New Zealand 1-1 Slovakia

Karawa tsakanin New Zealand da Slovakia
Image caption wasu magoya bayan Slovakia suna murnar kwallon da suka ci

An ta shi daya daya tsakanin New Zealand da Slovakia a wasan da suka buga a rukunin F.

Hakan dai na nufin yanzu kowacce kasa na da maki dai dai a rukunin, wanda ya kunshi mai rike da kanbun Italiya da kuma Paraguay.

Slavakia ne dai suka fara zura kwallo a wasan jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kuma haka su kayi ta kai hare-hare domin neman kara wasu kwallayen, sai hakarsu bata cimma ruwa ba.

Yayinda a mintunan karshe dan wasan New Zeland Reid ya farke mata kwallon.

Kuma wannan itace kwallo ta farko da kasar ta ci a gasar cin kofin duniya cikin shekaru 28, kuma shi ne maki na farko da samu atarihin ta.