Za a mayar da magoya bayan Argentina 17 gida

Dandazon magoya bayan Argentina
Image caption Argentina ta yi kaurin suna wajen fadace-fadace afilayen wasa

Mahukunta a Afrika ta Kudu za su mayar da magoya bayan Argentina 17 gida, bayan da aka same da laifin tada hankali a lokacin gasar cin kofin duniya.

An bayyana su a matsayin barazana ga jama'a wadanda ka iya kawo cikas ga gasar.

Mutanen na daga cikin 'yan kallo 800 da mahukunta a Argentina suka haramtawa kallon kwallo a kasar, sannan aka mika sunayen su zuwa jami'ai a Afrika ta Kudu.

Akwai dai wasu karin magoya bayan Argentinan biyar da suka fice daga Afrika ta Kudu a kashin kansu.

'yan sanda ne dai suka kama mutanen awani sumame da suka kai ranar Laraba a garin Pretoria inda masu sha'awar kwallon kafa 165 suke zaune.