An sabunta: 16 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 11:57 GMT

Karawa tsakanin Spaniya da Switzerland

Wasu daga cikin tawagar 'yan kwallon Spaniya

Wasu daga cikin tawagar 'yan kwallon Spaniya

Bayan rawar da ta taka a shekaru biyun da suka gabata, Spaniya na da kwarin guiwar taka rawar azo agani a gasar ta bana.

Kuma nasarar da suka samu da ci 6-0 a kan Poland ta nuna yadda suka shiryawa gasar, bayan dawowar Fernando Torres da Cesc Fabregas, wadanda suka yi fama da rauni.

Alamar tambaya daya ce kawai ta rage kan Andres Iniesta, duk da cewa kociya Vicente del Bosque, ya ce dan wasan na Barcelona zai warke a kan lokaci, amma har yanzu yana gwaji ne cikin taka-tsan-tsan.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Itama Switzerland tana fama da matsalar rauni, Alexander Frei da Valon Behrami, ba za su taka leda ba, abinda ya sanya kociya Ottmar Hitzfeld sauya tunani.

Daga cikin 'yan wasan da ake saran za su taka rawar gani sun hada da Cesc Fabregas a bangeren Spaniya, da kuma Philippe Senderos a daya bangaren.

Switzerland ta shafe mintuna 394, ba tare da an sakamata kwallo a gasar cin kofin duniya ba, kuma Spaniya ce kasa ta karshe data zira mata kwallon a gasar 1994 a Amurka.

Ana ta bangaren Spaniya na daga cikin kasashe na gaba-gaba da ake saran za su lashe gasar baki dayan ta.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.