Argentina 4 Koriya ta kudu 1

Argentina ta doke Koriya
Image caption Argentina ta doke Koriya

Argentina ta doke Koriya ta kudu da ci hudu da guda a wasan da kasashen biyu suka buga a rukunin B.

Dan wasan Argentina Gonzalo Higuain ya zura kwallaye uku a wasan.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci dai an tashi wasan ne ci biyu da guda.

A yanzu haka dai Argentina nada maki shida ne a rukunin B, bayan ta lashe wasanni biyu, sai kuma Koriya ta Kudu tana maki uku bayan nasarar da ta yi akan Girka da ci biyu da nema a wasan farko da ta buga.