Karawa tsakanin Girka da Najeriya

Karawa tsakanin Girka da Najeriya
Image caption Karawa tsakanin Girka da Najeriya

Bayan wasan farko da kasashen biyu suka buga wanda kuma aka doke su, Najeriya da Girka na neman nasara domin samun tsallakewa zuwa zagaye na biyu a rukunin B.

A wasan farko da Najeriya ta buga da Argentina a rukunin, ta sha kashi ne da ci daya da mai ban haushi a yayinda ita kuma Girka ta sha kashi da ci biyu da nema a hannun Koriya ta Kudu.

Kasashen biyu sun hadu sau biyu a baya inda Najeriya a doke Girka a gasar cin kofin duniya da aka shirya a Amurka a shekarar 1994, a wasan Najeriya ta doke Girka da ci biyu da nema. Sai kuma wasan sada zumunci inda Girkan ta doke Najeriya a shekarar 1999.

Tamkar duk wanda aka doke a wasan na yau zai kwashe kayansa ya koma gida.