Girka 2-1Najeriya

Karawa tsakanin Najeriya da Girka
Image caption A yanzu zai yi wuya Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na gaba

Kasar Girka ta doke Najeriya da ci 2-1 a karawar da suka yi a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

A minti na 16 ne dan wasan Najeriya Uche ya fara zira kwallo bayan wani firi kik da aka buga.

Sai dai 'yan wasan Najeriyar sun fara gazawa bayan da alkalin wasa ya kori Sani Kaita, bayan da ya taka dan wasan Girka dagan-gan.

Abinda ya baiwa Girkan damar mamaye wasan, inda ta kuma rama kwallon ta mintuna biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan andawo Girka ta ci gaba da kai hare-hare, amma sai a minti na 72, sannan suka samu kan su inda suka zira kwallo ta biyu.

Yanzu dai sai awasan karshe sannan za a san makomar Najeriya, ganin cewa Argentina wacce ta lashe wasanni biyu, ta tsallake zuwa zagaye na biyu.