An sabunta: 18 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:42 GMT

Sloveniya 2-2 Amurka

Amurka ta farfado daga kwallon biyun da aka zira mata, inda ta ta shi biyu da biyu tsakanin ta Slovaniya, a rukunin C.

Ba a dade da fara wasa ba Slvaniya ta zira kwallon farko ta hannun dan wasan ta Birsa a minti na 13, sannan ta kara ta hannun Ljubijankic a minti na 43.

Amma ana dawowa daga hutun rabin lokaci sai Amurka ta rama kwallon daya a minti na 48 ta hannun

Landon Donovan.

Kafin Bradley ya zira kwallo ta biyun ana saura minti takwas a tashi wasa.

Wannan wasa dai ya baiwa Amurka kwarin guiwa a kokarin da take yi na tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

A yanzu dai Sloveniya nada maki hudu, yayinda Amurka take da maki biyu.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.