Italiya 1-1 New Zealand

Italiya da New Zealand
Image caption Italiya da New Zealand

An yi canjaras da ci daya da daya tsakanin kasashen New Zealand da Italiya a cigaba da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Afrika ta Kudu.

Kasar New Zealand ce ta fara samun nasara a kasa da mintina goma na farkon wasan, yayinda kasar Italiya ta farke kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kowanne bangare yayi ta kai kora, amma har aka tashi babu wacce ta sake samun damar sake zura kwallo.

Wannan wasa dai na daga cikin irin abubuwan mamaki da suke faruwa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Afrika ta Kudu.

Kasashen da ake gani a da suna da karfi sosai yanzu da kyar suke sha a hannun kasashen da a baya ba a lissafi da su sosai a harkar kwallon kafa.

Kamar Ingila ita ma Italiya ta yi kunnen doki har sau biyu, wanda hakan na iya jefa su cikin hadari idan basu yi nasara ba wasansu na gaba.

Masana kwallon kafa dai na ganin cewa New Zealnd din ta yi rawar gani sosai a wannan wasa.