Italiya 1 New Zealand 1

Italy ta buga kunnen doki da New Zealand
Image caption New Zealand ta yi ba zata a wasan

New Zealand ta buga kunnen doke da Italiya a yayinda suka tashi daya da daya a wasan na biyu da suka buga a rukunin F.

Dan wasan New Zealand Shane Smeltz ya zura kwallon farko, bayan minti bakwai da fara wasan, kafin kuma Riccardo Montolivo ya fanshewa Italiya kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A yanzu haka dai Italiya mai rike da kambun tana da maki biyu a rukunin bayan wasanni biyu da ta buga. Ita ma New Zealand tana da maki biyu ne.

Paraguay dai ce ke jogoranci a rukunin da maki hudu a rukunin bayan ta doke Slovakia da ci biyu da nema.