An sabunta: 21 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:39 GMT

Chile 1-0 Switzerland

Chile

Magoya bayan Chile na murnar nasarar da suka samu

Chile ta doke Switzerland da ci daya mai ban haushi, a karawar da suka yi a rukunin H, wanda ya sata kasancewa kan gaba a rukunin.

Wasan ya dauki wani salo na musamman ne bayan da alkalin wasa ya kori Behrami na Switzerland a minti na 31.

Daga nan ne kuma Chile ta mamaye wasan inda tayi ta kai munanen hare-hare.

Haka nan kuma su kaita fuskantar tirjiya daga 'yan bayan Switzerland har a ka tafi hutun rabin lokaci a ka dawo.

Sai a minti na 75 ne dan wasan Chile Gonzalez ya zira kwallon da ta raba bangarorin biyu.

Duk da korafin cewa yayi satar gida da 'yan bayan Switzerland suka yi alaklin wasa ya karbi kwallon.

A yanzu dai Chile ce kan gaba a wannan rukuni da maki shida, yayinda Switzerland ke biye mata da maki uku, sai Spaniya da Honduras suna nema.

An jima kadanne dai Honduras za ta kara da Spaniya, kuma duk wanda aka doke a wasan to sai dai ya san inda dare yayi masa.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.


BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.