Spaniya 2 Hunduras 0

Spain ta barar da kwallaye da dama a wasan
Image caption Spain ta barar da kwallaye da dama a wasan

Spaniya ta doke Hunduras da ci biyu da nema a wasa na biyu da kasashen biyu suka buga a rukunin H.

David Villa ya zura kwallon farko cikin minti goma sha bakwai da fara wasan. Sanan kuma da aka dawo hutun rabin lokaci dan wasan ya zura ta biyu ana minti biyar daga dawowa.

David Villa ya samu bugun daga kai sai mai tsaron gida amma dai ya barar. Spaniya ta barar da kwallaye da da dama a wasan.

A yanzu haka dai Spaniya da Switzerland na da maki uku ne yayinda Chile ke da maki shida a rukunin bayan ta doke Switzerland da ci daya mai ban haushi.