An sabunta: 22 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 17:36 GMT

Karawar karshe a rukunin B

Najeriya da Jamhuriyar Korea Republic za su kece raini a karo na farko a gasar cin kofin duniya.

A gasar da aka shirya a Jamus a shekarar 2006 Koriya ta kara da Togo inda tayi galaba akanta da ci biyu da guda.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Najeriya kuma wannan ne kuma zai zama karo na farko da za ta kara da wata kasa daga nahiyar Asiya a gasar cin kofin duniya.

Najeriya za ta nemi ta zura kwallon guda a ragar Koriya kuma tayi fatan Argentina ta doke Girka.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Argentina dai ta rika ta tsallake zuwa zagaye na gaba, kuma kocin kasar Diego Maradona ya ce ba zai yi amfani da wasu daga cikin 'yan wasan ba.

Najeriya dai bata da maki a rukunin, yayinda Koriya da Girka ke da maki uku kowannen su. Ita kuma Argentina tana da maki shida ne.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.