An fitar da Afrika ta Kudu

Magoya bayan Afrika ta Kudu
Image caption Magoya bayan Afrika ta Kudu jim kadan kafin kammala wasan

An fitar da mai masaukin baki Afrika ta Kudu daga gasar cin kofin duniya, duk da nasarar da ta samu a kan Faransa.

Afrika ta Kudun ta doke Faransa da ci 2-1, amma sai dai hakan yayi kadan, ganin cewa Uruguay ta samu nasara a kan Mexico da ci 1-0.

A binda yasa duka Afrika ta Kudu da Faransa za su san inda dare yayi musu.

A yanzu dai Uruguay ce ta lashe wannan rukuni da maki bakwai, yayinda Mexico ke biye da ita da maki hudu, sai dai ba'a samata kwallaye da yawa kamar Afrika ta Kudu ba.

Kawo yanzu dai ta zamo kasa ta biyu daga cikin kasashen Afrika baya ga Kamaru, da aka fitar a gasar, kuma wasu na ganin hakan ka iya yin tasiri wajen armashin gasar a tsakanin 'yan kasar ta Afrika at Kudu.