An sabunta: 23 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 09:34 GMT

Karawar karshe a rukunin C

A yau za a yi ta ta kare a rukunin C wanda ya kunshi Ingila da Aljeriya da Amurka da Slovaniya, inda kowa keda damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Slovaniya na fatan kafa tarihi a karawar da za su yi da Ingila, nasara ka iya baiwa kasar damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Sai kociyan Ingila Fabio Capello ba zai so ganin hakan ta faru ba, musamman ganin irin fatan da 'yan kasar keda shi a kan kungiyar, idan har aka doke Ingila to zai zamo karo na farko da aka fitar da ita a rukunin farko tun 1958.

Kasashen biyu za su kara ne a filin wasa na Port Elizabeth, kuma yayainda Ingila ke neman nasara domin ta tsallake, ita kuwa Slovaniya kunnen doki ma kawai ya isar mata.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Wasa na biyu

A daya wasan na rukunin C, wanda za a buga lokaci guda, Algeriya za ta kara da Amurka inda kowanne ke fatan samun nasara domin tsallakewa.

Idan har aka ta shi kunnen doki a wannan wasan to Amurka ka iya tsallakewa, musamman idan aka doke Ingila, idan kuwa Ingila ta tashi kunnen doki, to yawan kwallaye ne zai rabata da Amurka.

Yayinda Aljeriya ke fatan samun nasara da akalla kwallaye biyu, idan har ta tanason takai labari.

Aljeriya za ta zamo kasa ta hudu da za ta san matsayin ta a nahiyar Afrika, bayan da aka fitar da Kamaru da Afrika ta Kudu da kuma Najeriya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.