An sabunta: 24 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:26 GMT

Karawar karshe a rukunin E

Bayan da Holland ta riga ta tsallake zuwa zagaye na biyu, kuma jirgin 'yan Kamaru ke jiran su a tasha, hankali zai karkata ne kan Japan da Denmark.

Duka Japan da Denmark na bukatar nasara ne domin kaiwa ga gaci, ganin cewa dukkan su na da maki uku uku, bayan da suka doke Kamaru, sannan suka sha kashi a hannun Holland.

Kociyan Denmark Morten Olsen ya zargi 'yan wasansa da gazawa a karawar da suka yi da Kamaru, kuma ya sha alwashin ganin sun gyara matsalar a karawar ta yau.

Denmark din dai za ta dogara ne kan Bendtner da Dennis Rommedahl domin neman nasara.

Sai dai yayin da Denmark ke fatan samun nasara ido rufe, ita kuwa Japan gaba ta kaita domin koda an tashi kunnen doki, to itace za ta kai labari.

Idan har Japan ta tsallake, to za ta zama kasa ta biyu bayan Koriya ta Kudu daga nahiyar Asiya data tsallake zuwa zagaye na biyu.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Wasa na biyu

Karawa tsakanin Kamaru da Holland dai ba ta da wani mahimmanci sosai ganin cewa tuni aka riga aka fitar da Kamaru daga gasar.

Yayinda a bangare guda Hollad ta riga ta tsallake zuwa zagaye na biyu.

Ana saran shahararren dan wasan Holland Ian Robben zai taka leda a yau bayan da yasha fama da rauni, abinda kuma ya hanashi buga wasannin da aka yi a baya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.