An fitar da Italiya a gasar cin kofin duniya

Italiya da Slovakiya
Image caption Wannan ne karo na farko da aka fitar da Italiya a zagayen farko cikin shekaru masu yawa

An fitar da mai rike da kanbun kofin kwallon kafa na duniya Italiya, bayan da ta sha kashi ahannun Slovakiya da ci uku da biyu.

Wannan ne karo na uku da aka fitar da mai rike da kambun gasar a zagayen farko, kuma ba karamin koma baya bane ga kasar ta Italiya.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ne Slovakiya ta zira kwallon farko, sannan suka kara ta biyu bayan an dawo.

Italiya ta rama kwallo daya bayan da wasa yayi wasa, sannan ta ci gaba da kai hare-hare, amma sai Slovakiya ta zira kwallo na uku ana gab da tashi.

Kafin daga bisani Italiya ta kara zira kwallo daya a karin lokaci.

A yanzu dai Paraguay da Slovakiya ne suka tsallake zuwa zagaye na biyu. Paraguay ta tashi daya da daya a wasanta da New Zealand.