Brazil da Portugal sun tsallake zuwa zagaye na biyu

Karawa tsakanin Brazil da Portugal
Image caption Duka bangarorin biyu sun zubar da damarmaki masu yawa

Brazil da Portugal sun tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

An dai ta shi babu ci ne tsakanin kasashen biyu, abinda ya nuna cewa an fitar da Ivory Cost daga gasar.Ita dai Ivory Cost ta so Brazil ta doke Portugal ne sannan ita kuma ta samu damar tsallakewa.

Ivory Cost ta doke Koriya ta Arewa da ci uku da nema, kuma koda an doke Portugal to ba za ta tsallake ba, domin kwallaye tara take bukata.

Wannan sakamakon na rukunin G ya nuna cewa a yanzu kasar Ghana ce kawai ta tsallake zuwa zagaye na biyu daga cikin kasashe shidan da suka fito daga nahiyar Afrika.