An sabunta: 27 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 15:24 GMT

Karawa tsakanin Argentina da Mexico

Kasashen biyu sun hadu ne a zagaye na biyu a gasar da aka shirya a Jamsu a shekarar 2006 inda Argentina ta yi nasara a kan Mexico da ci biyu da guda.

Mexico dai za ta nemi ta rama abin da Argentina ta yi mata a shekarar 2006.

Argentina dai ce ta jagoranci rukunin B a gasar ta wannan shekara sai kuma Mexico ta zamo na biyu a rukunin A.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Argentina dai tana da zaratan 'yan wasan karkashin jagorancin Diego Maradona amma haryanzu dai gwarzon dan kwallon duniya, Lionel Messi bai zura kwallo ba a gasar cin kofin duniya.

Ita ma dai Mexico za ta taka rawar gani ganin irin wasannin da ta buga a zagayen farko a rukunin A.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.